21 Satumba 2025 - 08:28
Source: ABNA24
Sojojin Isra'ila Sun Kai Munanan Hare-Hare A Gaza; Shahidai 110 Cikin Sa’oi 24 + Bidiyo

Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan gidajen Falasdinawa da ke kusa da masallacin Al-Aybaki da ke unguwar Al-Tuffah da ke gabashin Gaza. A lokaci guda kuma jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da munanan hare-hare a wasu unguwanni da ke cikin birnin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Tun da sanyin safiyar yau ne dai birnin Gaza ya fuskantar hare-hare masu yawa daga sojojin Isra'ila. A tsakiyar birnin, sojojin mamaya sun yi luguden wuta da manyan bindigu a unguwannin da ke kusa da titin Al-Nafaq. Har ila yau, a unguwar Al-Darj, sun kai wani hari ta sama a wani rukunin gidaje da ke kusa da mashigar Al-Sha’biyya, wanda ya yi sanadin shahadar akalla mutane hudu tare da jikkata wasu da dama.

Arewa maso yammacin Gaza kuma an samu munanan fashe-fashen bama-bamai, inda sojojin Isra'ila suka tayar da wasu motoci masu sulke da bama-bamai a cikin yankunan da al’umma ke rayuwa da kuma kusa da hasumiyar Al-MuKhabirat. Hotunan da aka fitar daga wannan aiki sun nuna mugwinya da tashin hankali na waɗannan fashe-fashe.

A gefe guda kuma, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi luguden wuta kan unguwar Sheikh Radwan da ke arewa maso yammacin Gaza da kuma kusa da mahadar Al-Ghafri. A sa’I daya shima wani jirgin sama mai saukar ungulu na Apache na Isra'ila shi ma ya bude wuta kai tsaye a gabashin birnin Gaza.

Sannan wani harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan wani tsagin gini da ke unguwar Sabra da ke Gaza ya yi sanadiyyar shahidai 17 tare da bacewar wasu da dama

Yayin da majiyoyin Falasdinawa suka bayar da rahoton shahadar al'ummar Gaza 110 cikin sa'o'i 24 zuwa safiyar yau Lahadi, mummunan harin da Isra’ila ta kai a tsakar daren Asabar a wani katafaren gidan da ke kan titin Al-Maghrib da ke unguwar Sabra a kudancin birnin Gaza ya yi sanadiyar shahada akalla 17 ya zuwa yanzu, kuma har yanzu mutane da dama na makale a karkashin baraguzan hare-haren.

Majiyoyin Falasdinawa sun wallafa hotunan tarin gawarwakin shahidai a asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza cikin sa'a da ta wuce.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha